12 Yuli 2021 - 12:25
​Iran Ta Yi Allawadai Da Halartar Taron Kungiyar MKO Da Firai Ministan Kasar Slovenia Ya Yi

Gwamnatin kasar Iran ta yi allawadai da firaiministan kasar Sloveniya wanda ya halarci taron kungiyar ‘yan ta’adda masu adawa da jumhuriyar musulunci ta Iran, wacce aka fi sani da MKO.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya ce ministan ya yi allawadai da halattan taron wanda Firai ministan ya yi, wanda kuma aka gudanar ta yanar gizo a jiya Lahadi. Zarif ya bayyana haka ne a zantawarsa ta wayar tarho da shugaban kungiyar tarayyar Turai Josept Borrel a jiya din.

Zarif ya kara da cewa dole ne kungiyar tarayyar turai (EU) ta bayyana matsayinta dangane da abubuwan da Firai ministan ya fada a taron, don shi ne yake rike da shugabancin kungiyar ta EU na karba–karba a halin yanzu.

A maida martani Josept Boreel ya fadawa Zarif kan cewa firai ministan Sloveniya ba ya wakiltar kungiyar tarayyar Turai EU a taron na kungiyar yan ta’adda masu adawa da JMI wacce aka fi sani da MKO. Kuma maganganun da ya yi a taron ba ra’ayin kungiyar ne dangane da kasar Iran ba.

Banda haka ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a nan birnin Tehran ta kira jakadiyar Slovenia da ke nan Tehran zuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar don bayyana korafinta kan halattar taron na MKO da kuma jawaban da Firaministan kasarta ya yi.

342/