ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya nakalto Abbas Gholroo ya nafadar haka a jiya A sabar a lokacinda yake ganawa da mai bawa shugaban kasar Siriya shawara kan al-amuran yankin yammacin Asia Bethenatu Sha’aban.
Gholroo ya kara da cewa ya na da kyau kasashen biyu sun karfafa dangantaka a tsakaninsu, wadanda suka hada da na addini, al-adu da kuma Tarihi.
A nata bangaren Bethenatu Sha’aban ta bayyana cewa a halin yanzu, tsaron kasar Siriya ya na hannun sojojin kasar da kuma mutanen kasar Iran ne wadanda suke yakar ‘yan ta’adda tare.
Mai bawa shugaban kasar Siriya shawara kan al-umuran yankin Asia ta kuda ta kammala da cewa gwamnati da mutanen kasar Siriya ba za su taba mantuwa da kasar Iran ba saboda gudumawar da ta bayar, har da na rayuka don kare kasar ta Siriya daga makiya.
342/