20 Yuni 2021 - 11:48
Shuwagabannin Kasashen Duniya Sun Fara Taya Zababebben Shugaban Kasar Iran Murnar Zabensa

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya mika sakon taya murna ga zababben shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi a wani sakon da ya aikewa ofishin jakadancin kasar Iran dake birnin Mosco a yau Asabar.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press ya ce Putin a cikin sakon ya kara jaddada irin dangantaka mai karfi wacce take tsakanin kasashen biyu. Ya kuma yi fatan za su yi ayyuka wadanda za su kawo ci gaban kasashen biyu da zabebben shugaban kasar.

Har’ila yau tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cewa shugaban kasar Siriya Bashar Al-asad ya mika sakon taya murnar zaben Sayyid Ibrahim Ra’isi a matsayin sabon shugaban kasar Iran.

A wani labarin kuma shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabi Beri ya aike da sakon taya murna ga zabebben shugaban kasar na Iran Sayyid Abrahim Ra’isi.

342/