ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana haka ne a safiyar yaua Talata ta kuma kara da cewa mutanen da sunayensu suka fito a jerin ‘yan takaran dai sun hada da Saeed Jalili, Seyyed Ebrahim Raeisi, Mohsen Rezaei, Alireza Zakani, Seyyed Amir-Hossein Ghazizadeh-Hashemi, Albdolnasser Hemmati, da kuma Mohsen Mehr-Alizadeh.
Ma’aikatar ta kara da cewa mafi yawan mutane 592 wadanda suka yi rijistan sunayensu don shiga takarar shugabancin kasar basu bada cikekken takardun da ake bukatar su bayar ba. Don haka daga cikinsu mutanen 40 ne kacal suka bada cikekken takardunsu, amma daga karshe an fitar da mutane 7 wadanda zasu shiga takarar shugabancin kasar a ranar 18 ga watan yuni mai zuwa.
Fitattu daga ‘yan takarar dai sun hada da Sayyeed Ibrahim Ra’isi alkalin alkalan kasar a halin yanzu, Saeed Jalili, Mohsen Rezaei da kuma gwamnan babban bankin kasar Abdonnasir Himmati.
342/