ABNA24 : Bayanai sun ce jama’a sun fito a Paris, inda hukumomin suka haramta yin zanga zangar, inda akayi ta dauki ba dadi tsakanin masu zanga zangar da ‘yan sanda a wasu sassan birnin birnin.
A wasu sassan kuma an gudanar da zanga zangar ba tare da wata hatsaniya ba.
A wani labarin kuma an gudanar da zanga zangar ta goyan bayan al’ummar Falasdinu a birnin London na Biritaniya, inda masu zanga zangar suka nufi ofishin jakadancin Isra’ila dauke da tutocin Falasdinu.
342/