ABNA24 : Za’a kwashe kwana biyar ana karbar takardun takara masu sha’awar tsayawa a zaben shugabancin kasar.
Bayan kammalar rejistar majalisar da aka dorawa alhakin tantance ‘yan takara a zabe, zata bayyana sunayen wadanda aka amince da takararsu a zaben shugaban kasar wanda shi ne karo na 13, tun bayan juyin juya halin musulinci na kasar.
Wadanda aka zaba a matsayin ‘yan takarar zaben Shugaban Kasa karo na 13 za su shiga yakin neman zabe a lokacin da aka tsara a ranar 28 ga watan Mayu har zuwa 17 ga watan Yuni mai zuwa.
Kafin hakan ministan cikin gida na kasar ta Iran ya kira zaben mai zuwa a matsayin mai ciki da muhimmanci.
Abdolreza Rahmani Fazli ya ce za a gudanar da zaben cikin aminci da tsaro.
342/