ABNA24 : Mahmood Vaezi ya kara da cewa har yanzun dai muna iya cewa babu wani abu wanda zai iya zama barazana ga tattaunawar gaba dayanta. Kuma tattaunawar ta na tafiya bisa yadda tawagar Junhuriyar Musulunci ta Iran ta tsara.
Idan har wannan halin ya ci gaba muna iya cewa akwai fatan za’a cimma matsaya guda nan gaba.
Babban abinda kasar Iran take bukata a wannan tattaunawar dai shi kafin Amurka ta dawo cikin yarjejeniyar to dole ne ta daukewa Iran dukkan takunkman tattalin arzikin da aka dora mata bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar a shekara ta 2018.
342/