13 Afirilu 2021 - 12:52
Turkiyya Da Libiya Sun Cimma Yarjejeniyoyi Da Dama

Kasashen Turkiyya da Libiya, sun sanar da cimma yarjeniyoyi da dama a tsalaninsu.

ABNA24 : Kasashen biyu sun sanar da hakan ne yayin taron manema labarai da suka jagoranta a jiya Litini, yayin ziyara da firaministan Libiya ya kai Turkiyya.

Shugaba Recep Erdogan, na Turkiyya, ya sha alwashin murtunta hurimin Libiya.

Ya kuma sanar da cimma yarjejeniya da Libiyar, ta fuskar soji akan abunda ya kira kawo karshen zubar da jinni, da kuma kaucewa faduwar birnin Tripoli.

Haka kuma kasashen biyu sun cimma yarjejeniya a fuskar kiwon lafiya, da tattalin arziki, inda Turkiyya ta yi alkawarin zubar da jari a fannoni daban daban a kasar Libiya.

Shi kuwa firaminsitan na Libiya, ya bukaci goyan bayan Turkiyya domin tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma taimakawa sake gina kasar Libiya.

342/