ABNA24 : Daga cikin abubuwan da shugaba Muhammad Bazoum ya yi alkawalin bai wa muhimmanci a lokacin mulkinsa da akwai bunsa harkokin ilimi, tsaro da kuma fada da cin hanci da rashawa.
Sabon shugaban na jamhuriyar Nijar ya ce; “Duk wani mai rike da mukamin gwamnati shi ne ke da alhakin duk abinda ya aikata, kuma iyalansa da jam’iyyarsa ta siyasa ko alumma ba za su taimaka masa ba.”
Wani sashe na jawabin shugaba Muhammad Bazoum ya kunshi cewa; Hanya mafi dacewa ta fada da cin hanci da rashawa ita ce ta hukunta wadanda aka tabbatar sun aikata, don haka ba zan daurewa kyale wadanda su ke cin hanci da rashawa cikin walwala ba.
A jiya jumaa ne dai aka rantsar da sabon shugaban kasar ta Nijar, Muhammadu Bazoum, inda aka sami halartar shugabannin kasashe da gwamnatoci da manyan baki daga kasashen da dama.
342/