ABNA24 : Tashar talabijin ta Almayadin ta kasar Lebanon ta nakalto shugaban yana fadar haka a safiyar yau Laraba, a taron majalisar ministocin kasar na karshe a wannan shekara ta 1399 mai karewa.
Rouhani ya kara da cewa shekara ta 1400 mai shigowa da yardarm All.. shekara ce ta budi a fagen bunkasan tattalin arziki a kasar Iran, ya ce shekarar mai karewa shekara ci mai tsanani ga Iraniyawa saboda matsalolin tattalin arziki mai tsanani da aka fuskanta da kuma annobar korona wacce lashe rayukan dubban mutanen kasar daga ciki har da na jami’an kiwon lafiya 270.
342/