23 Faburairu 2021 - 11:12
Gwamnatin Iran Ta Yi Maraba Da Umurnin Imam Khamina’e Na Daga Murya Gaba Daya Na Bukatar A Dagewa kasar Takukuman Tattalin Arziki

Gwamnatin kasar Iran ta bayyana anniyarta na ganin an daga murya guda a duk fadin kasar don ganin an kawo karshen takunkuman zalunci da Amurka ta dorawa kasar. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto wani bayanin da gwamnatin kasar ta fitar a yau wanda yake maraba da umurnin Imam Aliyul Khaminae na yin haka.

ABNA24 : Imam Khamina’e ya bayyana haka ne a jiya litinin a lokacinda ya ke ganawa da majalisar zaben jagora a nan birnin Tehran.

Bayanin ya kara da cewa gwamnatin kasar zata aiwatar da umurnin dakatar da amfani da bangaren kari na yarjejeniyarta da hukuma IAEA mai sanya ido kan shirye-shiryen makamashin nukliya na kasar saboda jawo hankalin dayan bangaren ya cika alkawarinsa a yau Talata.

342/