ABNA24 : Rahotanni daga kasar Iraki na cewa, a jiya Juma’a dakarun hadin gwaiwa na kasar da suka hada da sojoji da kuma dakarun sa kai na Hashd Al-shaabi, sun samu nasarar halaka wasu ‘yan ta’addan ashirin da biyu a farmakin da suke kaddamarwa.
Wannan na zuwa ne a cikin farmakin da sojoji da kuma dakarun sa kai na kasar suka fara kaddamarwa ne a kan ‘yan ta’adda da suke neman sake farfadowa a cikin kasar tare da taimakon wasu kasashen ketare.
Bayan halaka wannan adadi na ‘yan ta’adda, an kuma samu wasu daga cikin kayayyakin da suke amfani da su wajen kai hare-haren ta’addanci, da suka hada da bindigogi da kuma nakiyoyi gami da motoci masu sulke.
342/