ABNA24 : Zanga zangar dai na zuwa ne kwana guda bayan da matakin sanya kungiyar cikin jerin ‘yan ta’adda ya soma aiki, a daidai kuma lokacin sabon shugaban Amurkar Joe Biden, ya yi rantsuwar kama aiki.
A halin da ake ciki dai sabuwar gwamnatin Amurka, ta ce zata duba wannan batun cikin gaggawa, saboda fargabar tabarbarewar al’amuran jin kai a kasar ta Yemen da yaki ya daidaita.
Kasar Yemen, ta fada cikin yaki ne tun bayan da Saudiyya da kawayanta suka farma wa Yemen da yaki a cikin shekarar 2015.
Lamarin dai ya jefa kasar Yemen, cikin hali mafi muni a duniya, inji MDD, bayan haddasa hasarar rayukan dubban mutane da tilastawa milyoyin jama’ar kasar kaura.
342/