4 Disamba 2020 - 17:03
Iran Ta Gano Wasu Mutane Dake Da Hannu A Kisan Fakhrizadeh

Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta bayyana gano wasu mutane dake da hannu a kisan masanin nukiliyarta, Mohsen Fakhrizadeh.

ABNA24 : Da yake sanar da hakan, kakakin ma’aikatar leken asirin kasar ta Iran, ya ce an gano mutanen dake da hannu a kisan masanin nukiliyar, wadanda suka shigo da wasu kayayaki da na’urori da akayi amfani dasu wajen aiwatar da kisan a cikin kasar.

Koda yake labarin bai bayyana mutum nawa ne, amma ya ce, daga cikin mutanen akwai wadanda suka shigo da wasu na’urorin da kuma wadanda sukayi aiki da fasahohi.

A ranar Juma’a data gabata ne masanin nukiliyar kasar ta Iran, Mohsen Fakhrizadeh, ya yi shahada a wani hari da aka kai masa a wajen birnin Tehran, wanda mahukuntan kasar ta Iran suka dora alhakin hakan ga makiyyan kasar a sahun gaba Isra’ila, tare da sha alwashin maida martani a lokacin da ya dace.

342/