21 Nuwamba 2020 - 16:01
Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya Ya Kore Zargin Da Gwamnatin Habasha Ta Yi Masa Na Taimaka Wa “Yan Awaren Tigray

Shugaban hukumar lafiya ta duniya ( WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus wanda dan asalin yankin ne na Tigray, ya karyata zargin da sojojin Habasha su ka yi masa na cewa yana taimakawa ‘yan awaren.

ABNA24 : A jiya Alhamis ne dai Habasha ta sanar da cewa; sojojinta sun sami nasarori akan ‘yan awaren na yankin Tigray saboda sun karaci birnin Mekelle da shi ne babban birnin yankin.

Adhanom Ghebreyesus ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; “ Wasu rahotanni suna zargina da taimakawa wani gefe daya a halin da ake ciki. To wannan ba gaskiya ba ne,abinda kawai zan iya fada shi ne ina tare da zaman lafiya.”

Shugaban hukumar Lafiyar ta duniya ya kara da cewa:Zuciyata ta karaya matuka saboda abinda yake faruwa a kasata Habasha, don haka ina yin kira ga dukkanin bangarorin da su yi aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya da kuma tabbatar da kare lafiyar fararen hula.

342/