18 Nuwamba 2020 - 17:30
An Yi Girgizar Kasa Mai Karfin Ma’aunin Richter 4.5 A Kudancin Iran

Girgizan kasar mai karfin ma’aunin Richter 4.5 ta aukawa lardin Sistan Buluchistan da ke kudu masu gabacin kasar Iran. Rahotannin da suke fitowa daga cibiyar gwaje-gwajen girgizan kasa ta kasa, dake jami’ar Tehran ya bayyana cewa, girgizan kasar ta auku ne da misalign karfi 2 da mintuna 11 da sekan 9 na safiyar Laraba.

ABNA24 : Labrain ya kara da cewa girgizan ta auku ne kilomita 9 daga garin Galmurti na lardin sistan-Bulucsan, kuma tana da zurfin kilomiya 13 karkashin kasa. Ya zuwa lokacin bada wannan labarin dai babu bayani dangane da irin asarorin rayuka da dukiyoyin da girgizan kasar ta haddasa.(19)

342/