7 Nuwamba 2020 - 12:03
Zarif Ya Isar Kasar Cuba A Ziyarar Karfafa Alaka Da Yake Yi A Yankin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya isa kasar Cuba don ganawa da jami’an kasar a kokarin kasashen biyu na karfafa alakar da ke tsakaninsu da kuma tsara hanyoyin fada da takunkumin da Amurka ta sanya musu.

ABNA24 : Jaridar gwamnatin kasar Cuban Granma, ta sanar da cewa a jiya ne ministan harkokin wajen na Iran ya isa birnin Havana, babban birnin kasar Cuban inda ya gana da takwararsa na kasar Bruno Rodriguez don kara karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu da suke fuskantar takunkumin Amurka mai tsanani sakamakon kin mika mata kai da suka yi, inji jaridar.

Jaridar ta ci gaba da cewa: Kasar Kuba dai tana goyon bayan amfani da makamashin nukiliya a yanayi na zaman lafiya wanda hakki ne na kowace kasa, kamar yadda kuma ta yi Allah wadai da ficewa daga yarjejeniyar nukiliyan da Amurka ta yi.

Har ila yau jaridar tace tana da cikin ayyukan da Mr. Zarif zai yi har da tattaunawa kan hanyoyin da za a karfafa alaka ta kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.

Ministan harkokin wajen na Iran ya isa kasar Cuba din ne bayan ziyarar da ya kai kasar Venezuela inda ya gana da manyan jami’an kasar ciki kuwa har da shugaban kasar Nicolas Maduro.

342/