27 Oktoba 2020 - 11:16
​Baqeri: Amurka Ta Kuskura Ta Takali Iran Da Yaki Tsaida Shi Ba A Hannunta Yake Ba.

Babban hafsan hafsoshin sojojin Iran Manjo Janar Mohammad Baqeri ya bayyana cewa idan gwamnatin Amurka ta kuskura ta farwa kasar Iran da yaki, to kuwa kawo karshen yakin ba a hannunta yake ba. Don sanin haka ne take fakewa da yake-yaken wakilci a yankin don kada a ga hannunta ta kai tsaye a cikinsu.

ABNA24 : Majiyar muryar JMI ta nakalto Manjo Janar Baqeri yana fadar haka a safiyar yau Litinin a wani taro a nan birnin Tehran.

Ya kuma kara da cewa sojojin kasar Iran, a mahangar shirin kare kai, da tsoratar da makiya, da kuma hadin kai tsakaninsu, suna cikin kekyawan shiri.

Baqeri ya kara da cewa, bukatar Amurka a wajen Iran a fili yake, kuma shi ne mika kai ga bukatunta gaba daya. Wato ta zama ita ce take sarrafa kasar yadda take so.

Dangane da takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar kuma, Baqeri ya ce, a halin yanzu mutane da kuma gwamnatin kasar Iran sun maida takurawan da Amurka takewa kasar, a matsayin dama ta bunkaci kamfanonin cikin gida, wanda ya kasance babban nasara ga kasar.

342/