Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Ma'aikatar da ta bayyana damuwarta kan matsalolin bayar da agajin gaggawa, ta sanar da cewa, har yanzu adadi dayawa na wadanda abin ya shafa na ci gaba da kasancewa a karkashin baraguzan gine-gine ko kuma kan tituna a yashe, kuma jami'an agaji da na farar hula ba su samu isa gare su ba saboda tsananin tashin bama-bamai.

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da karuwar adadin shahidan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ke kai wa zirin Gaza, tare da sanar da cewa Palasdinawa 53,655 ne suka yi shahada tun farkon wadannan hare-hare a ranar 7 ga Oktoban 2023.
Your Comment