20 Mayu 2025 - 23:28
Source: ABNA24
Alaƙa Tana Ƙara Tsamari Tsakanin Birtaniya Da Isra'ila

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya: Mun dakatar da tattaunawa da gwamnatin Isra'ila kan yarjejeniyar cinikayyar makamai. Kafa Kasar Falasdinu shine mafuta

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: "David Lammy" ya fada a cikin wani jawabi a zauren majalisar dokokin Burtaniya a yau Talata:

Yayin da gwamnatin Netanyahu ke aiwatar da munanan manufofin siyasa a Yammacin Kogin Jordan da Gaza, ba za a iya samun ci gaba kan tattaunawar cinikayya cikin 'yanci ba. Domin idan Isra'ila ta ci gaba da ayyukan soji kuma ba ta ba da tabbacin isar da kayan agaji, za mu kara daukar mataki a kansu.

Lallai ne shirin Isra'ila ba zai kawar da Hamas ba kuma ba zai samar da tsaro ba

Gwamnatin Netanyahu ta mayar da Isra'ila saniyar ware daga kawayenta tare da lalata muradun al'ummar Isra'ila.

Matakin da muka dauka na dakatar da siyar da makamai ga Isra'ila yana da mahimmanci. Amincewa da kasar Falasdinu zai kasance mafi muhimmanci yanke shawara da muka yanke kuma zabar lokacin da ya dace don ita yana da matukar muhimmanci.

Za mu ci gaba da goyon bayan samar da zaman lafiya na kasashe biyu, wanda shi ne kawai tsarin samar da zaman lafiya mai dorewa

Ana haka kuma Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta soki matakin da Birtaniyya ta dauka

inda ta mayar da martani ga matakin na Birtaniya ta dauka da cewa: Idan har gwamnatin Burtaniya, saboda kyamar Isra'ila da kuma ra'ayoyin siyasar cikin gida, a shirye take ta cutar da tattalin arzikin Birtaniyya, to wannan shawarar wani lamari ne na su kadai.

Takunkumin da Landan ta kakaba wa matsugunan Isra'ila bai dace ba kuma abin takaici ne. Domin Wa'adin Burtaniya ya ƙare tun shekaru 77 da suka gabata.

Gwamnatin Birtaniya ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu jiga-jigan siyasa da cibiyoyin gwamnatin Sahayoniya da ke yammacin gabar kogin Jordan

Gwamnatin Burtaniya ta sanya takunkumi kan wasu mutane bakwai da hukumomi da suka hada da jam'iyyar Nahala da kamfanin gine-gine da ababen more rayuwa na LIBI a yammacin gabar kogin Jordan.

Aiwatar da takunkumin da aka kakaba wa matsugunin Zohr al-Sobh saboda shiga cikin aikatawa da kuma tallafawa ayyukan ta'addanci a kan Falasdinawa a Yammacin Kogin Jordan. Kakaba takunkumi kan matsugunan Yamma da Kogin Jordan na Niriya da mazaunanta saboda shiga cikin take hakkin dan Adam.

Bayan hakan Birtaniya ta gayyaci jakadan gwamnatin Isra'ila 

Ma'aikatar harkokin wajen Burtaniya ta sanar da cewa, ta gayyaci jakadan Isra'ila a kasar tare da sanar da shi cewa yarjejeniyar cinikayya makamai da gwamnatin kasar tana gab da dakatar da ita.

Shi ma sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy ya jaddada dangane da haka: "A yau mun dakatar da tattaunawa da gwamnatin Isra'ila kan yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci, kuma ba zai yiwu a ci gaba da tattaunawa kan wannan batu da gwamnatin da ke aiwatar da manufofinta na musamman a yammacin kogin Jordan da zirin Gaza ba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha