21 Mayu 2025 - 18:44
Source: ABNA24
Sojojin Isra'ila Sun Buɗe Wuta Ga Jami'an Diflomasiyya 30 Na Turai Da Ƙasashen Larabawa

sojojin Isra'ila ne sun buɗewa jami'an diflomasiyyar ƙasashen Turai da na larabawa su 30 a Jenin a yammacin gabar kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Bayan faruwar hakan kasashen da kungiyoyi dama sun fitar da da sako suna masu sukar wannan mummunan aiki da suka mai gauni. Kasashen Turai sun yi suka ta farko ga Isra'ila bayan harbin jami'an diflomasiyya

Manyan jami'an kasashen Turai sun bukaci Isra'ila ta yi masu bayani cikin gaggawa game da lamarin bayan harbin da sojojin Isra'ila suka yi ga wata tawagar diflomasiyya da ta kunshi jakadu da wakilan kasashen Larabawa da na Turai a ziyarar da suka kai sansanin Jenin.

Babban jami'in kula da harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai Kaya Callas ya bayyana a taron manema labarai a yau cewa: "Muna bukatar a gudanar da bincike cikin gaggawa kan wannan lamari, muna kuma sa ran za a hukunta wadanda suka aikata wannan laifi. Ba za a amince da barazanar da ake yi wa jami'an diflomasiyya ba, musamman daga ɓangaren da ke da hannu a yarjejeniyar Vienna, kuma tana da hakkin kare jami'an diflomasiyya".

Shi ma ministan harkokin wajen Italiya Antonio Tajani ya sanar a cikin wani sako ta kafar sada zumunta ta X cewa, ya tattauna da mataimakin karamin ofishin jakadancin kasar a birnin Kudus, inda ya bukaci a yi karin bayani cikin gaggawa game da harbin. Tajani ya rubuta cewa: Ba za a yarda da barazanar ga jami'an diflomasiyya ba kuma dole ne Isra'ila ta bayyana dalilin yin hakan.

A wani yunkuri da ba a taba ganin irinsa ba, sojojin Isra'ila sun bude wuta kan tawagar diflomasiyya da ta kunshi jakadu da dama da wakilan siyasa daga kasashen Larabawa da na Turai a ziyarar da suka kai sansanin 'yan gudun hijira na Jenin da ke gabar yammacin kogin Jordan; Matakin da ya fuskanci martani mai zafi daga ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu da kuma yin kira da a dauki mataki na duniya gaba ɗaya.

Ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu ta fitar da wata sanarwa a hukumance, ta dauki wannan yunkuri a matsayin misali karara na tsoratarwa da barazana ga jami'an diflomasiyya na kasa da kasa tare da yin Allah wadai da shi.

Kungiyar Hamas ta fitar da sanarwa kan harbin jami'an diflomasiyya da sojojin Isra'ila suka yi a Jenin

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matakin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka dauka na harbin jami'ai da jakadun kasashen Larabawa da Turai 30 a sansanin Jenin da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta bayyana matakin a matsayin wata alama ta "Jijidakai da girman kai na gwamnatin mamaya" da kuma keta dokokin kasa da kasa.

Sanarwar ta ce ci gaba da kai hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa Jenin a wata na biyar a jere, tare da ta'addanci a Tulkarm da Nablus da ake ci gaba da yi, wani bangare ne na yunkurin gwamnatin kasar na aiwatar da shirye-shiryen mamayewa da tilastawa Falasdinawa kauracewa gidajensu da kuma fadada matsugunan haramtacciyar kasar Isra'ila.

Ƙasar Faransa ta sanar da gayyatar jakadan Isra'ila a birnin Paris bayan harbin da sojojin Isra'ila suka yi wa tawagar diflomasiyya a Jenin.

Ƙasar Italiya ita ma ta gayyaci jakadan Isra'ila da ke Rome don samun cikakkun bayanai game da abubuwan da suka faru a Jenin.

Your Comment

You are replying to: .
captcha