ABNA24 : Kafafen watsa labarun ‘yan sahayoniyar sun ci gaba da cewa;A jibi Lahadi ne kwamitin da yake tsara gine-gine a yammacin kogin Jordan zai yi zama domin tattauna shirin gina gidaje 4500.
Majiyar ta kara da cewa; Fira Minista Benjamine Netenyahu ne ya bayar da umarnin a ci gaba da gina matsugunan ‘yan share wuri zauna a yankin na yamamcin Kogin Jordan.
Har ila yau, majiyar ta ce; Dama an tsayar da gina matsugunan ne saboda bayar da damar kulla alaka da kasashen larabawa, yanzu kuma da aka cimma manufa za a dora ginin daga inda aka tsaya.
Gina matsugunan yahudawa ‘yan share wuri zauna dai yana cin karo da kudurorin MDD akan Palasdinu.
342/