ABNA24 : A zaman mako guda kotun ta (ICJ), za ta duba ko tana da karfin gudanar da shari’ar, da Amurka ke ci gaba da kalubalanta.
A watan Yuli na shekara 2018 ne Iran, ta kai karar gwamnatin shugaba Donald Trump, kan sake kakaba mata takunkuman da aka dage mata wadanda suka jibanci yarjejeniyar nukiliyar data cimma da manyan kasashen duniya a shekara 2015.
Iran dai na mai bukatar kotun data dakatar da takunkuman na Amurka, har sai an ga yadda shari’ar ta kaya.
A watan Mayu na shekara 2018 ne shugaba Trump, ya sanar da janye kasarsa daga yarjejeniyar nukiliyar ta Iran.
A shekara 2018 dai Kotun ta ICJ, mai matsayin kotun koli ta MDD, ta bukaci Amurka data daga wasu daga cikin takunkuman data kakaba wa Iran, wadanda suka hada dana kaddarorinta a matsayin jin kai bisa tanadin yarjejeniyar amintaka ta 1955 dake tsakanin kasashen biyu, saidai daga bisani Amurka ta janye jiki daga yarjejeniyar.
342/