1 Satumba 2020 - 10:29
​Tawagar Gwamnatin Yahudawan Isra’ila Ta Isa Abu Dhabi Na UAE

A jiya ne tawagar gwamnatin yahudawan Isra’ila ta isa birnin Abu Dhabi fadar mulin kasar Hadaddiyar Daular Labawa UAE, bayan da bangarorin biyu suka sanar da kulla alaka a bayyane, bayan kwashe tsawon shekaru masu yawa suna hulda a boye.

ABNA24 : Tawagar gwamnatin yahudawan wadda ta isa birnin Abu Dhabi tare da wasu jami’an gwamnatin Amurka, ta hanyar sararin samaniyar kasar Saudiyya, ta samu tarba daga mahukuntan kasar UAE a birnin Abu Dhabi.

Shugaban majalisar tsaro ta gwamnatin yahudawan Isra’ila Ben Shabat ne ya jagoranci tawagar, wanda ya bayyana ranar ta jiya a matsayin ranar tarihi, yayin da a nasu bangaren mahukuntan UAE suka bayyana shirinsu na bunkasa alakarsu da gwamnatin yahudawan Isra’ila adukkanin bangarori na siyasa da tsaro da tattalin arziki da sauransu.

Sai dai a nasa bangaren Firai ministan Haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya yi wasu kalamai a jiya da suke a matsayin dizga mahukuntan UAE, bayan da suka bukaci Amurka ta sayar musu da jiragen yaki samfurin F-35 a sakamakon kulla alaka da Isra’ila a bayyane.

Netanyahu ya fito ya bayyana cewa, babu batun sayar wa UAE da jiragen yakin F-35 a cikin yarjejeniyar da suka kulla da UAE, haka nan ya karyata kalaman da mahukunatn UAE suka na cewa wannan yarjejeniyar za ta kawo karshen shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin Kogin Jordan, inda Netanyahu ya ce wannan ba gaskiya ba ne, domin kuwa yana nan kan bakansa na ci gaba da mamaye yankunan Falastinawa.

Ziyarar tawagar gwamnatin yahudawan zuwa Abu Dhabi ta zo ne adaidai lokacin da Isra’ila take kara tsanata hare-haren da take kaddamarwa a cikin kwanakin nan a kan yankin zirin Gaza.

342/