12 Agusta 2020 - 10:02
Nijar : An Fadada Dokar Ta-baci Bayan Harin Tillaberi

Gwamnatin jamhuriyar Nijar, ta sanar da fadada dokar ta baki a yankin Tillabery, kwanaki kadan bayan da wasu ‘yan bindiga suka kashe wasu ma’aikatan agaji guda takwas ciki har da faransawa shida.

ABNA24 : Haka kuma gwamnatin ta sanar da rufe wurin yawan bude idon na Koure inda aka kai harin, da kuma fadada dokar ta baci zuwa lardinan Kollo da kuma Baleyara.

Gwamnatin ta sanar da hakan ne bayan wani taron gaggawa na kwamitin tsaron kasar da Shugaba Isufu Mahammadu, ya jagoranta a jiya Litini.

Babu dai wata kungiya da ta fito fili ta dauki alhakin kai harin, saidia yankin na Tillaberi ya yi kaurin suna wajen fuskantar hare haren mayakan dake ikirari da sunan jihadi musamman a iyakokin Nijar din da Mali da kuma Burkina Faso.

A wata sanarwa da jagorar kungiyoyin agajin kasa da kasa reshen Nijar, ta fitar, ta ce harin da aka kai a yankin Koure ba zai katse masu hamzarin gudanar da ayyukansu ba, hasali ma zai kara masu kuzari.

Kasashen NIjar da Faransa dai sunyi tur da harin suna masu danganta shi da na ta’addanci tare da shan alwashin gudanar da bincike domin zakulo wadanda suka aikata shi domin gurfafanar dasu gaban kuliya.

342/