2 Agusta 2020 - 11:00
An Zabi Iran Domin Shugabancin Kwamitin Kula Da Mahalli Na MDD, Duk Da Barazanar Amurka

An zabi Jamhuriyar musulinci ta Iran, da gagarimin rinjaye domin shugabancin hukumar zartaswa na kula da mahalli na MDD.

ABNA: Iran dai za ta shugabancin wannan hukuma na tsayon wa’adin shekara guda daga 2020-2021.

Ma’aikatar harkokin wajen Iran, ta ce ba’a zamu wata turjiyya ba wajen amincewa wa Kasar shugabancin wannan hukuma duk da barazanar Amurka.

Amurka dai ta yi barazanar ficewa da kuma dakatar da bada tallafinta ga hukumar ta MDD mai kula da mahalli muddin aka zabi Iran din domin jagorancin hukumar

342/