ABNA24: Mai magana da yawun rundunar sojin yahudawan Isra’ila Afikhay Adrai ya bayyana cewa, sojin ya halaka ne a lokacin da sojojin yahudawan suke gudanar da wani atisayi a kusa da iyakar kasar Lebanon, bayan da wata motar soji mai sulke ta wuntsile da su, inda a nan take sojin na sra’ila ya halaka, wani kuma ya samu raunuka.
Bayan faruwar wannan lamari dai sojin na Isra’ila sun dakatar da atisayin wanda suka fara a jiya, inda suke gwada karfinsu a kan iyakar kasar Lebanon da Falastinu.
Wannan dai yana zuwa sakamakon tsoron da yahudawa suka shiga a cikin yankunan Isra’ila, bayan da jiragen yakin Isra’ila da suka kai hari a cikin kasar Syria a ranar Litinin da ta gabata, suka kashe daya daga cikin dakarun Hizbullaha cikin kasar at Syria, inda yahudawa ke cikin zullumi da tsoro, saboda rashin sani dangane da irin martanin da kungiyar ta Hizbullah za ta mayar kan hakan.
Sojojin an Isra’ila dai suna gudanar da atisayin ne a kusa da iyakokin kasar Lebanon, domin kwantar da hankulan sauran yahudawa da suke cikin zaman zullumi da tsoro, kan martanin da suke zaton cewa Hizbullah za ta mayar a kansu.
342/