ABNA24: Kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a taron kwamitin yaki da cutar Korona a kasar a safiyar yau Asabar.
Shugaban ya kara da cewa ya zuwa yancu cutar korona ta kashe mutane dubu 14 a kasar sannan adadin wadanda suka kwanta a asbiti ya kai 200,000 sai dai nan gaba hasashen ya nuna cewa adadin zai ninka.
Shugaban Rouhani ya ce kasar Iran tana da magunguna cutar korona har guda biyar, sannan a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa za ta fara amfani da wani sabo.
Daga karshe shugaban ya kammala da cewa akwai hasashen mutane miliyon 30-35 zasu kamu da cutar nan gaba.
Yawan mutanen da suka kamu da cutar a cikin yan makonnin da suka gabata a nan birnin Tehran ya kara yawa, wanda hakan ya tilastawa gwamnatin kasar sake rufe wasu wuraren harkokin kasuwanci a wannan kano, wadanda ba’a dade da budesu ba.
342/