13 Yuli 2020 - 11:50
Iran : Jagora Ya Bukaci A Kara Hadin Kai Domin Dakile Annobar Covid-19

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, ya bukaci al’ummar kasar dasu kiyaye matakan kiwan lafiya da aka gindaya domin dakile yaduwar cutar korona a kasar.

(ABNA24.com) Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bukaci ko wanne mahaluki ya bada himma domin murkushe yaduwar cutar cikin sauri, domin ceto kasar.

Jagoran ya bayyana hakan ne ta kafar bidiyo a lokacin da ya ke ganawa da sabbin ‘yan majalisar dokokin kasar da suka kama aiki a karshen watan Mayun da ya gabata.

A wani bangare na jawabinsa, wanda shi ne na farko ga ‘yan majalisar dokokin kasar, Jagoran ya jinjinawa ma’aikatan lafiyan kasar akan yadda suka sadaukar da kansu, a yayin da kuma ya soki wadanda a cewarsa suka kasa biyaya ga matakan dakile cutar inda ya bayar da karamin misali na sanya takunkumin rufe fuska da wasu basa yi.

Hukumomin kiwon lafiya a Iran, sun bayyana cewa mutane 194 ne suka rasa rayukansu a cikin sa’o’I 24 da suka gabata sai kuma 2,186 da suka harbu da cutar.

A jimillance mutum 257,000 ne suka kamu da cutar a fadin kasar tun bayan bullarta a watan Fabrairu, a yayin da jimmilar wadanda cutar ta yi ajalinsu ya kai 12,829.

342/