1 Yuli 2020 - 12:35
Fashewar Tukunyar Iskar Oxygen Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 19 A Wani Asbiti A Anan Tehran

Kakakin ma’aikatar yan kwanakwana a nan birnin Tehran ya bayyana cewa fashewar wata cilindar iskar Oxygen a wani asbiti a arewacin birnin Tehran ta yi sanadiyyar tashin gobara a asbitin da kuma mutuwar mutane 19 da kuma raunata wasu 14.

(ABNA24.com)  Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto Jalal Maliki ya na cewa ma’aikatansa sun sami nasarar kubutar da mutane 20 wadanda suke cikin dakin da abin ya faru. Kuma sun kashe gobarar da ta taso a asbitin mai benaye.

Daga cikin wadanda suka ji rauni an yiwa mutane 7 magani a nan take, amma sauran mutanen 7 suna jinya a asbitoci a birnin.

Tuni dai shugaban kasa Iran Dr Hassan Rouhani ya bukaci a gudanar da bincike don sanin yadda hatsarin ya auku.

342/