(ABNA24.com) Jaridar Isra’ila ta Israel Hayom ta bayar da rahoton cewa, ana gudanar da wata tattaunawa a cikin sirri matuka, tsakanin jami’an gwamnatocin Amurka, Saudiyya da kuma Isra’ila kan batun Quds.
Jaridar Israel Hayom ta yahudawan Isra’ila, wadda ake bugawa a cikin harshen Hebru, ta bayar da rahoton cewa, wasu majiyoyin gwamnatin Isra'ila sun tabbatar mata da cewa; ana gudanar da wata tattaunawa a cikin sirri, tsakanin jami’an gwamnatocin Amurka da Saudiyya da kuma Isra’ila kan batun masalalcin Quds.
Rahoton jaridar yahudawan ya ce, kasantuwar gwamnatin Saudiya daya daga cikin bangarorin da suke mara baya ga shirin yarjejeniyar karni ta Donald kan makomar Falastinu, a halin yanzu Amurka da Isra’ila suna kokarin ganin sun saka Saudiyya a cikin kwamitin kula da harkokin masallacin Quds, wanda kasar Jordan ce da Falastinawa suke tafiyar da kwamitin.
Jaridar ta ce, wannan yana daga cikin shirin Isra’ila na mamaye wasu yankunan kasar Jordan da suke iyaka da yankunan Falastinawa, da kuma sauran yankunan falastinawa da ke yammacin kogin Jordan, wanda tun a cikin watan Disamban 2019 ne bangarorin uku suka fara tattaunawa kan hakan.
Kamfanin dillancin labaran Falastina na MA’A ya bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin Saudiyya sun tabbatar masa da cewa, da wuya gwamnatin kasar Jordan ta amince da wannan shiri, musamman yadda ta nuna yin watsi da shirin mayar da yankunan Falastinawa na gabar yamma da kogin Jordan a karkashin Isra’ila.
/129
2 Yuni 2020 - 04:06
News ID: 1042482

Jaridar Isra’ila ta Israel Hayom ta bayar da rahoton cewa, ana gudanar da wata tattaunawa a cikin sirri matuka, tsakanin jami’an gwamnatocin Amurka, Saudiyya da kuma Isra’ila kan batun Quds.