28 Afirilu 2020 - 04:42
 An Fara Yakin Neman Zabe A Kasar Burundi A Yau Litinin

An kaddamar da yakin neman zaben shugaba da na ‘yan majalisun dokoki da kananan hukumoki na kasar Burundi, a yau Litinin.

(ABNA24.com) Bude yakin neman zaben dai yana zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da rashin gaskata juna a tsakanin gwamnati da al’ummar kasar akan yadda ta ke tafiyar da yaki da cutar corona.

Za a ci gaba da yin yakin neman zaben dai daga nan har zuwa ranar 17 ga watan Mayu,kamar yadda wata doka da shugaban kasar ya rattabawa hannu ta amince.

Za a gudanar da manyan zabuka ne a cikin kasar ta Burundi a ranar 20 ga watan Mayu mai zuwa.

Da akwai ‘yan takara 7 da za su yi gogayya akan kujerar shugabancin kasar ta Burundi da su ka hada da dan takarar da jam’iyya mai mulki ta tsayar CNDD- FDD, wato Janar mai ritaya Evariste Ndayishimiye, da zai maye gurbi shugaban kasar mai ci Pierre Nkurunziza.

Jam’iyyar adawa ta CNL ta tsayar da fitaccen dan siyasa kuma tsohon dan tawaye mai wakiltar kabilar Hutu, Agathon Rwasa.


/129