(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen kasar ta Iran Muhammad Jawad Zarif, ya isa birnin Damascuss ne a jiya Litinin, inda ya fara ganawa da manyan jami’anta da su ka hada da shugaban kasa Basshar Assad.
Tattaunawar bangarorin biyu dai ta mayar da hankali ne akan hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labarun “SANA” na kasar Syria ya nakalto shugaba Basshar Assad yana cewa; Matsalar Corona da ta kunno kai, ta bayyana hakikanin gwamnatocin kasashen turai ta yadda kare wasu tsirarun mutane ne ya dame su, ba kare dukkanin al’ummarsu ba.
Har ila yau shugaba Basshar Asad ya yi suka akan halayyar Turkiya ta kin aiki da yarjejeniyar Astana wacce ta kunshi yin furuci da kasancewar Syria kasa daya dunkulalliya.
A nashi gefen, ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya yi suka akan yadda kasashen turai din su ke son dawo da batun amfani da makamai masu guba a kasar Syria, da kokarin damfara shi ga gwamnatin kasar.
/129
22 Afirilu 2020 - 05:29
Lambar labari: 1028473
Ministan Harkokin Wajen Iran Da Yake Ziyarar Aiki A Kasar Syria Yana Ci Gaba Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasar