(ABNA24.com) Wannan shi ne mataki mafi tsauri wanda gwamnatin kasar Italiya ta dauka bayan kasar Cana inda cutar ta fara bulla. Firai ministan kasar ta Italiya Giuseppe Conte ne ya bada wannan sanarwan a jiya Lahadi bayan mutuwar mutane 366 a lokaci guda sabuda cutar.
A halin yanzu dai an hana shiga ko fita daga jihohi da kuma garuruwa 14 sai tare da izini. Har’aila yau an rufe dukkan wuraren taruwa wadanda suka hada da makarantu filayen wasanni, hotel-hotel da wuraren shakatawa a duk fadin kasar.
Sanarwan rufe wadannan yankuna ta ce wannan halin zai ci gaba har zuwa 3 ga watan Afrilu mai zuwa, kafin a sake duba al-amarin .
Ya zuwa yanzu dai cutar ta Corona ta kama mutane fiye da dubu 100 a duk fadin duniya, amma dubu 55 daga cikinsu sun warke sannan 3500 kuma suka rasa rayukansu.
/129