8 Janairu 2020 - 16:56
Jagora : Martani Mai Tsanani yana Zuwa

Ayatullah Sayyid Ali Khamna’I jagoran juyin musulunci na iran yace; martani mai tsanani na nan tafe akan Amruka wannan somun tafi ne

Taskar watsa Labarai ta Ahlul-Baiti{a.s}ABNA- ta lakanto jagoran juyin musulunci a jawabin da ya gabatar a yau Laraba , Ayatullah Khamna’i, ya ce wannan harin, somun tabi ne ga Amurka, don kuwa martanin kisan Janar Shahid Qasim Suleimani na zuwa a nan gaba.

Ayatullah Khamna’i, ya kara da cewa, ba wai Iran din da aka sani ba ce a shekara 1977, yanzu Iran ta mallaki makamman kare kai fiye da yadda ake tsammani don fuskantar abokan gaba.

A cikin daren jiya ne dakarun kare juyin juya halin musulinci na Iran, sukayi ruwan makamai masu linzami kan sansanin sojin Amurkar guda biyu ciki har da na Ain Al’asad wanda shi ne babban sansanin sojin Amurka a Irakin.