17 Agusta 2017 - 09:34
Dakarun IRGC Na Iran Sun Sanar Da Shirin Daukar Fansa Kan 'Yan "Da'esh"

Kakakin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran (IRGC) Birgediya Janar Ramazan Sharif ya bayyana cewar za su dau fansa kan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) sakamakon kisan gillan da suka yi wa daya daga cikin dakarun kare juyin da suka kama a kasar Siriya ta hanyar yi masa yankan rago.

A wata hira da yayi da tashar talabijin din Al-Mayadeen ta kasar Labanon, Birgediya Janar Ramazan Sharif ya bayyana cewar dakarun IRGC din tuni suka fara aiwatar da wani shiri na daukar fansar jinin Shahid Mohsen Hojajji da sauran dakarun da suka tafi Siriya da nufin kare wajaje masu tsarki na kasar da kuma taimakon gwamnati a fadar da take yi da ta'addanci.

Har ila yau Janar Sharif ya ce dakarun kare juyin dai ba za su taba yin kasa a gwiwa wajen kare dakarun kare juyin da suke tafiya kasar Siriya a matsayin masu ba da shawara ga sojojin Siriyan a fada da suke yi da 'yan ta'addan ba yana mai cewa dakarun na su ba sa gudanar da ayyukansu su kadai ba tare da hadin gwiwan gwamnatin Siriyan ba.

A kwanakin baya ne dai 'yan kungiyar ta'addancin ta Da'esh suka watsa wasu faifan bidiyo na irin azabar da suka yi wa shahid Mohsen Hojajji din bayan da suka kama shi kafin daga baya kuma suka masa yankan rago.288