15 Mayu 2025 - 16:36
Source: ABNA24
Mutane 100 Su Kai Shahada A Hare-Haren Da Isra'ila Ta Kai Gaza A Yau

Mutane 100 ne sukai shahada a hare-haren da Isra'ila ta kai a Gaza tun daga safiyar yau

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (A.S.) - ABNA - ya habarta cewa: Kafofin yada labaran Falasdinu na cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban-daban na zirin Gaza; hare-haren da sukai sanadiyar shahadar mutane sama da 100 ya zuwa yammacin yau, inda 61 daga cikinsu sun yi shahada ne a harin da aka kai wa Khan Younis.

Majiyoyin labarai sun ruwaito a safiyar yau cewa wasu gine-ginen gidaje da dama a yankin Mawasi da ke kudancin kasar, da garuruwan Qara da Abbasan al-Kabaira a arewa maso gabas, da Bani Suhayla da yankin Ma'an a gabas, da yankin al-Sakka da ke tsakiyar Khan Younis, jiragen yakin Isra'ila da jirage masu saukar ungulu ne suka kai hari a ci gaba da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila taje kaiwa ga al'ummar Falasɗinu.

Your Comment

You are replying to: .
captcha