Shugaban cibiyar neman jaririn watan a gundumar Yazd ya sanar da tura kungiyoyin kwararru hudu zuwa sassan daban-daban na gundumar domin ganin jaririn watan.
A yau juma'a ne Hujjatul-Islam Ali Ridha Sharifi ya fadawa kamfanin dillancin labarun Irna cewa; A cikin wadannan gungu-gungu na mutane,da akwai kwararru 20 da su ka hada masana ilimin falaki.
Mutanen za su zauna a kauyukan Ardkan, Mubid, da kuma wani sashe na kauyen Taft domin sa ido akan fitowar jaririn watan gabanin faduwar ranar yau juma'a.
Sharifi ya ci gaba da cewa; Saboda ba abu ne mai yiyuwa ba a iya ganin jaririn watan kai tsaye da idanu a gundumar ta Yazd, kungiyoyin za su yi amfani da na'urorin zamani na hangen nesa.
Kungiyoyin da su ke aiki a gundumar ta Yazd, suna a karkashin cibiyar ganin watan azumi ne ta kasa.288