Tsaron ke daukan wadannan matakan ba.
Me yasa canjin wajen ci gaba da tsaro alhali Kotu ta riga ta bada umurnin sakin Malam din cikin kwanaki 45? Sannan kuma wane tabbaci suke da shi na sabon wajen ta fuskar tsaron lafiyar Malam?.
Malam Badamasi Yakubu kanin Malam shakiki ne ya furta haka nan a wata ganawa da yayi da manema labarai bayan jin wannan sabon shirin na jami'an tsaro.
Kamar yadda aka sani dai a jiya Asabar ne wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa sojoji sun je sun kewaye gidan da ake tsare da Malam da iyalin sa Malama Zeenatuddeen Ibraheem, sannan kuma sun soma kwashe kayayyakin gidan da hujjar wai za'a canza masu wajen zama.
Saboda rashin tabbas game da tsaron lafiya Sheikh El-Zakzaky ya sa aka rika gangami na gaggawa a wajen Nigeria a birnin London da wasu kasashen musulmi.288