20 Mayu 2024 - 12:52
Za'a Gudanar Da Shirye-shiryen Jajantawa Da Jana'izar Shahid Ayatullah Raisi A Birnin Qum Da Mashhad.

Kamar yadda aka tsara a baya-bayan nan, za a gudanar da taron tunawa da shahidan masu tsarki ne wanda a halin yanzu aka mayar da shi ga rundunar Ashura da karfe 4:00 na yamma a garin Tabriz.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: A gobe da safe kuma za a gudanar da taron bankwana wanda al'ummar Tabriz zasu yi da Shahidai shugaban kasar da shahid limamin Juma'a abun kauna da kuma shahid gwamnan kasar Azarbaijan ta gabas, da kuma shahidan Husain Amirabdollahian da sauran shahidai.

Bayan mika shahidai zuwa birnin Tehran, jagoran juyin juya halin Musulunci zai yi gudanar da Sallah ga jikkunan shahidai masu tsarki a Laraba.

A cewar hukumar tsare-tsaren an yanke cewa, idan aka kammala shirye-shiryen, gawar shugaban shahidan za ta kasance bako a birnin Qum domin gudanar da dawafin zagawa da shi a hubbaren Sayyidah Fadima Ma'asumah Karimatu Ahlul Bauta As.

Za a yi jana'izar binne gawar shugaban Khadimul-Ridha a birnin Mashhad ranar Alhamis. Har ila yau, za a binne gawar fitaccen limamin Juma'a na Tabriz da kuma matashin gwamnan gabashin Azarbaijan a birnin Tabriz a ranar Alhamis