11 Yuli 2023 - 03:25
Yarjejeniyar Tsakanin Iran Da Iraki Don Ba Da Fasfo Na Musamman Ga Maziyarta Arbaeen

Sharadi na musamman na Arbaeen don masu tattakin Arbaeen Muharram 14444

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Sardar Ahmad Ali Gudarzi, kwamandan masu tsaron kan iyakar Faraja ya bayyana cewa: A jiya mun yi wata ganawa mai kyau da takwarorinmu na Iraki a gaban ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda muka yanke shawarori masu kyau. an yi su ne domin saukaka tafiyar maziyarta Arbaeen na Imam Husaini (AS).


Yayin da yake ishara da cewa gwamnatocin kasashen Iran da Iraki sun cimma yarjejeniya kan bayar da fasfo din Arbaeen na musamman, inda ya ce: an sami kyakkyawan tsarin tafiyar da Maziyarta da fitarsu, sufuri da walwala da ayyukan da maziyarta Arbaeen suke bukata.


Godarzi ya bayyana cewa an tanadi mafuta kan iyaka guda 7 ga maziyarta a lokacin Arba'in, Godarzi ya ce: an yi la'akari da iyakoki guda 7 don shiga da fita na maziyarta da gudanar jerin gwano, da kuma iyakoki 6 na shiga da fita na maziyarta wannan lamari dai ya nuna zurfin alaka da kokarin da kasashen biyu ke yi na saukaka zirga-zirgar maziyartan.