Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

21 Mayu 2022

15:15:31
1259534

Mutum Uku Sun Mutu Yayin Wani Harin Isra’ila A Siriya

Rahotanni daga Siriya na cewa mutane uku ne suka rasa rayukansu kana wasu hudu suka jikkata yayin wani harin makamai masu linzami da Isra’ila ta kai a kusa da birnin Damascos.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Majiyoyin tsaro daga Siriya sun ce Isra’ilar ta harba makamai ne tun daga yankin tuddan Golan da ta mamaye, an kuma samu barna sakamakon farmakin.

Kungiyar dake sanya ido kan harkokin kare hakkin bila dama ta OSDH, a Siriya, ta ce wadanda harin ya yi ajalinsu jami’an soji ne guda uku, sai kuma wasu sojoji hudu da suka jikkata.

An kuma samu tashin gobara a kusa da filin jirgin na Damascos.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Isra’ila ke kai irin wannan hari a Siriya ba, ko a ranar 13 ga watan nan wani harin ya kashe mutum 5.

342/