27 Yuli 2020 - 11:22
Na’eem Qasim:Shirin Daukar Fansa Kan HKI Yana Nan Kamar Yadda Yake

Mataimakin sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sheikh Na’eem Qasim ya bayyana cewa shirin daukar fansar shahidan kungiyar kan sojojin Isra'ila (HKI) ya na nan ba tare da wani sauyi ba. Sai dai kungiyar ce za ta bayyana lokaci da kuma irin fansar da zata dauka.

ABNA24: Sheikh Qasim ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Almayadeen a birnin Beirut babban birnin kasar ta Lebanin a jiya Lahadi da yamma.

Malamin ya kara da cewa idan HKI ta kuskara da farwa kasar Lebanon da yaki, to kuwa makomarta zai kasance kamar yadda yake a yakin shekara ta 2006 ne wato na kwanaki 33..

A wani wuri a maganarsa, Sheikh Qasim ya bayyana cewa kungiyar ta karbi sako daga HKI dangane da daukar fansan da za ta yi na kissan shahida Ali Kamil Muhsin wanda HKI ta yi a kasar Siriya, amma zabi ya na hannunta.

Har’ila yau sheikh Qasim ya yi allawadai da kokarin jawo hatsari ga jirgin saman fasinjan kasar Iran wanda sojojin Amurka suka yi a sararin samaniyar kasar Syriya, sannan ya bayyana cewa samuwarta a kasar ta Syriya bay a bisa ka;ida tun asali.

342/