ABNA24: Sheikh Qasim ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Almayadeen a birnin Beirut babban birnin kasar ta Lebanin a jiya Lahadi da yamma.
Malamin ya kara da cewa idan HKI ta kuskara da farwa kasar Lebanon da yaki, to kuwa makomarta zai kasance kamar yadda yake a yakin shekara ta 2006 ne wato na kwanaki 33..
A wani wuri a maganarsa, Sheikh Qasim ya bayyana cewa kungiyar ta karbi sako daga HKI dangane da daukar fansan da za ta yi na kissan shahida Ali Kamil Muhsin wanda HKI ta yi a kasar Siriya, amma zabi ya na hannunta.
Har’ila yau sheikh Qasim ya yi allawadai da kokarin jawo hatsari ga jirgin saman fasinjan kasar Iran wanda sojojin Amurka suka yi a sararin samaniyar kasar Syriya, sannan ya bayyana cewa samuwarta a kasar ta Syriya bay a bisa ka;ida tun asali.
342/