-
Malama Zeinat: Addinin Musulunci Zai Tabbata A Najeriya Masu Ikon Duniya Ba Za Su Iya Hana Hakan Ba
An gudanar da wani taron na tunawa da ranar shahadar Sayyida Fatima Zahra (A.S) a Tehran a ranar Litinin, wanda ya kunshi jawabi mai muhimmanci daga Malama Zeinatudden Ibrahim, matar Sheikh Ibrahim Zakzaky - shugaban Harkar Musulunci a Najeriya.
-
Labarai Cikin Hotuna: An Kaddamar Da Aikin "Barguna Ga Falasdinu" A Masallacin Claremont Da Ke Cape Town
An gayyaci mahalarta su dinka murabba'ai 15cm x 15cm a launukan Falasdinu. Kowane murabba'i yana wakiltar yara goma da aka kashe a kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a Gaza. Manufar wannan aiki ita ce a dinka murabba'ai 2,000, wanda ke wakiltar yara sama da 20,000 waɗanda aka ɓatar da rayukansu. Za a buɗe bargon Falasdinu da aka kammala a Ranar Nuna Goyon Baya ta Duniya ga Al'ummar Falasdinu, 29 ga Nuwamba, 2025.
-
Shugabannin Shi'a Sun Taru Don Tattaunawa Kan Zaɓen Firayim Ministan Iraki
An gudanar da taron "Shugabanin Tuntuba" na ƙungiyoyin Shi'a na Iraki a gidan Haider al-Abadi, tare da halartar Firayim Minista Muhammad al-Sudaani.
-
Bin Salman Zai Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Nukiliya A Tafiyarsa Zuwa Washington
Yariman Saudiyya mai jiran gado zai sanya hannu kan "Yarjejeniyar Tsarin Haɗin Kan Makamashin Nukiliya na zaman lafiya" a lokacin ziyararsa ta aiki a Amurka tare da Shugaban Amurka Donald Trump.
-
Labarai Cikin Hotuna: Koyar Da Littafin 'Arba'una Hadith' A Hussainiya Sheikh Zakzaky Da Ke Jos, Najeriya
A Hussainiya Sheikh Zakzaky da ke Jos, Sheikh Muhammad Auwal Abubakar ya gabatar da darasin Lahadi na mako-mako. Zaman na wannan makon ya mayar da hankali ne kan illolin Riya (bayyana aiki a cikin ibada) a cikin littafin Arba'una na Imam Khomeini Qs.
-
Riyadh: Shugaban Iran Ya Aikewa Da Yarima Saudiyya Saƙon Wasika
Hukumar Yaɗa Labarai ta Saudiyya ta sanar da cewa Yarima Mai Jiran Gado Na ƙasar ya karɓi saƙon rubutu daga Shugaban Iran.