(ABNA24.com) Shugaban Jamhoriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa magance matsalolin duniyar musulinci yana bukatar hadin kan kasashen musulmi da kuma aiki tare.
A yayin dake halartar taron birnin Kuala Lampur na kasar Malesiya, a wannan laraba shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rouhani ya gana da Sultan Abdallah sarkin kasar Malesiya inda ya ce katsa landan din da manyan kasashen Duniya ke yi a lamuran cikin gidan kasashen musulmi shi ne ya hana kasashen ci gaba, kuma a halin da ake cikin akwai bukatar hadin kai domin ci gaba a fanin ilimi da tattalin arziki.
Shugaba Rouhani ya yi ishara kan shekaru 70 da raba Al'ummar Falastinu da kasarsu, inda ya bukaci mahalarta taron kasashen musulmi dake gudana a birnin Kuala Lampur da su dauki matsalar Falastinu da mahimanci.
A nasa bangare Sultan Abdallah sarkin kasar Malesiya ya jinjinawa shugaba Rouhani da ya halarci wannan taro, tare da fatan All.. ya sanya wannan taro ya zamanto alheri ga al'ummar musulinci gaba daya.
Har ila yau Sultan Abdallah ya bayyana fatansa na karfafa alaka da kuma samun hadin kai a tsakanin kasashen musulmi.
/129
19 Disamba 2019 - 06:51
Lambar labari: 995047
Shugaban Jamhoriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa magance matsalolin duniyar musulinci yana bukatar hadin kan kasashen musulmi da kuma aiki tare.