9 Nuwamba 2019 - 04:41
An Ci Tarar Shugaban Kasar Amurka Dala Miliyan Biyu

Wata kotun Amurka a birnin New York ce ta yanke hukuncin cin tarar shugaban kasar Donald Trump dala miliyan biyu bayan da aka sami cibiyarsa ta ayyukan agaji da karya doka ta hanyar shiga harkokin zabe.

(ABNA24.com) Wata kotun Amurka a birnin New York ce ta yanke hukuncin cin tarar shugaban kasar Donald Trump dala miliyan biyu bayan da aka sami cibiyarsa ta ayyukan agaji da karya doka ta hanyar shiga harkokin zabe.

Shugaban na kasar Amurka ya yarda cewa cibiyar tashi ta agaji ta aikata ba daidai ba, tare da yin alkawalin kara sanya idanu akan ayyukanta anan gaba.

Mai shigar da kara ya bukaci ganin an kwace dala miliyan biyar daga asusun cibiyar, sannan kuma a kara da cin tarar ta wata dala miliyan biyu. Sai dai alkalin da ya yanke hukuncin ya yi watsi da bukatar farko amma ya amince da cin tarar cibiyar ayyukan agajin ta Donlad Trump.

A shekarar 2016 ne Donald Trump da ‘ya’yansa su ka karkata kudaden da suke asusun cibiyar ayyukan agaji ta Trump zuwa fagen yakin neman zabe, lamarin da ya sabawa dokokin zabe a cikin Amurkan.



/129