(ABNA24.com) A lokacin da yake ganawa da yan jami'yarsa ta AK a birnin Ankara shugaban kasar Turkaiya Dayyib Rajab Ardogan ya bayyana cewa ba zai taba tattaunawa da mayakan kurdawa ba har sai sun bar Arewacin kasar Siriya , kuma an kafa tudun mun tsira.
Ya kara da cewa akwai wasu shuwagabanin kasashe dake kokarin shiga tsakani na ganin an dakatar da bude wuta, su sani cewa bai taba ganin haka a tarihin kasar ba, ta zauna teburi daya da kungiyar yan ta’adda yana nufin mayakan kurdawa, don haka babu wani karfi da zai iya dakatar da hare haren sojin har sai sun cimma muradinsu,
Wannan yana zuwa ne bayan da Amurka ta kakabawa kasar turkiya takunkumi domin tilasta mata dakatar da kai hare haren, sai dai shugaban na turkiya yayi wasti da kiraye kirayen, yana mai cewa da zarar an samar da tudun muntsira a garin Manbij me nisan kilo mita 350 da kasar Iraki to zaa dakatar da kai hare haren,
/129