(ABNA24.com) Jam’iyar masu kishin musulinci ta Annahda a kasar Tunsiya ta samu nasarar lashe kujeru 57 daga cikin yawan kujeru 217 damajalisar dokokin kasarke da ita.
Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Tunusiya na cewa a zaben majalisar Dokokin da aka yi karshen makon da ya gabata, jam’iyar musulinci ta Annahda ce karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Rached Ghannouchi na samun yawon kujeru na ‘yan majalisar dokokin kasar, inda ta samu kuri’u kimanin 57 daga cikin yawan kujeru na Majalisar 217, bayanta kuma sai jam’iyar Qalbu Tunus karkashin Jagorancin Nabil Karoui kuma dan takara a zaben shugaba ta zo a matsayi na biyu da kujeru kimani 40.
A bangare guda kuma hakumar zaben ta kasar Tunisiya ta ce kimanin kashi 41,31 ne cikin dari suka kada kuri’unsu daga cikin mutanan da suka caccanci kada kuri’u a kasar.
Wannan zabe na ‘yan Majalisa shine karo na biyu, bayan da aka yiwa kundin tsarin milkin kasar Kwaskwarima, kuma shi ne zabe na uku bayan juyin juya hali da aka yi a kasar a shekarar 2011.
/129
12 Oktoba 2019 - 04:54
Lambar labari: 981851
Jam’iyar masu kishin musulinci ta Annahda a kasar Tunsiya ta samu nasarar lashe kujeru 57 daga cikin yawan kujeru 217 damajalisar dokokin kasarke da ita.