(ABNA24.com) Shugaban Jamhuriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa matsalolin yankin, kasashen yankin ne ya kamata su zauna kan teburi guda domin warware su.
Kafin barinsa birnin Tehran a daren jiya Lahadi zuwa birnin Ankara na kasar Turkiya da nufin halartar taron kasashen uku da suka hada da Rasha , Turkiya da Iran kan rikicin Siriya , Shugaba Rouhani na Iran ya ce kasancewar Amurka a yankin ya sabawa doka, kuma duk abubuwan da suke faruwa a yankin sakamakon katsalandan din da kasar Amurka ke yi a yankin ne.
A yayin da yake ishara kan hare-haren wuce gona da irin da kasashen Saudiya da hadaddiyar daular larabawa ke kaiwa kan kasar Yemen bisa goyon bayan Amurka, Shugaban na Iran ya ce wannan goyon ya yi sanadiyar salwanta dubban rayukan mutanen kasar yemen ba tare da sun aikata wani laifi ba.
Shugaba Rouhani ya kara da cewa; daga cikin muhimman batutuwan da za su tattauna kansu a taron na birnin Ankara, sun hada da ci gaba da yaki da ta'addanci, da kuma toshe duk wani taimako da 'yan ta'adda ke samu daga kasashen waje, da kuma sake gina kasar ta Siriya, tare da komawar 'yan kasar da suka yi hijra zuwa kasashen ketare gami da yadda za a yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima ta yadda za a gudanar da zabe a shekara ta 2021.
/129
16 Satumba 2019 - 08:48
Lambar labari: 975901
Shugaban Jamhuriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa matsalolin yankin, kasashen yankin ne ya kamata su zauna kan teburi guda domin warware su.